Ticker

6/recent/ticker-posts

Lagos: Farashin Rago ya kai naira miliyan ɗaya a kasuwar Alaba saboda yajin aikin masu kayan gwari

                                                           kasuwar alaba rago a legas


Farashin kayayyaki sun lunka kusan sau uku sakamakon yajin aikin.

Tanimu Bulama Wazirin Sarkin Alabar Rago kuma shugaban masu sauke dabbobi a kasuwar ya ce an taya wani ragonsa dubu 950 bai sayar ba.

Yan kasuwar sun ce kusan yawancin ragunan da su ke kaiwa kudancin Najeriya ana kawo su ne daga Sudan da Nijar.

Kaji da ake sayarwa N1,500 yanzu sun koma N2,500 sakamakon yajin aikin da ya haifar da ƙarancin kajin.

Ɗaya daga cikin ƴan kasuwar Alaba a ɓangaren kaji Muhammadun Dauran Kaji ya ce yanzu Talo-Talo har naira dubu 30 ake sayar da shi.

Muhammadu Aminu mai kayan gwari ya ce albasa da ake sayarwa N12,000 yanzu ta koma dubu 30 kwando.

Tumatur kuma da ake sayar wa naira hamsin yanzu sai dai kusan 300.

 

Abin da ƴan kasuwar suka ce kan yajin aikin

Shugabannin kasuwar sun ce suna yajin aikin ne domin neman wa ƴan uwansu ƴancinsu.

Sarkin kasuwar Alaba rago, Alhaji Umaru na Goggo ya musanta cewa an ɓoye kayyakin ne don a tsawalla farashi.

Ya kuma ce ko za a janye yajin aikin sai kungiya ta yi zama ta yi nazari kafn janye aikin.

"Sai mun yi zama da waɗanda abin ya shafa musamman jigogin gwamnati mun zauna da su a yi wa kafin kungiya ta amince a janye yajin aikin."

Sarkin kasuwar kuma ya n yi kira ga Gwamnatin Najeriya ta shiga tsakani ta yi bincike domin gano wadanda ke da gaskiya da kuma daukar mataki kan wadanda ke saɓa doka.

Tanimu Bulama Wazirin Sarkin Alabar rago shugaban masu sauke dabbobi a kasuwar ya ce baya ga nuna muhimmancin amfanin kasuwancinsu na kayayyakin abinci da suke kawo a kudanci suna kuma son a ɗauki mataki kan kuɗaden da ake tatsa daga gare su.

"Muna neman wa mutanenmu ƴancinsu ne kuma dole mu ba su yi hakuri su jure har lokacin da za a dadaita wannan al'amarin," in ji shi.

Ya ƙara da cewa wannan gargaɗi ne saboda fahimtar amfanin masu kawo kayan abinci a yankin kudancin Najeriya.

Post a Comment

0 Comments