A hira da shahararren mai daukan hoto da bidiyo wanda shine gogan mai daukar shirin wasan kwaikwayo na ‘Labarina’ Murtala Balala, ya bayyana cewa a tarihin farfajiyar fina-finan Kannywood, ba a taba shirya kasaitaccen shiri na wasan kwaikwayo wato (Series) kamar shirin Labarina ba.
Babala kwararren mai daukan bidiyo da hotuna ne wanda ake yi wa laƙabi da ‘WizKid’ saboda kwarewar sa a harkar sarrafa na’urar daukan hoto da bidiyo.
A hirar sa da PREMIUM TIMES, Balala ya ce ” Wannan shiri na labarina ya dauke hankalin mutane matuka a musamman yankin Arewa, da zaran lokacin shirin yayi zaka ga mutane na tururuwa, ana rige-rige, ana turereniya domin aje gaban Talbijin don kallon shirin.
Idan da za ka iya tunawa da fim din 24 wanda aka shirya shi a kasar Amurka wanda a lokacin da ake haska shi babu inda za ka leka ba za ka ga fim din ake kallo ba toh haka shirin Labarina yanzu a kasar nan da wasu kasashe dake makwabtaka da mu. Yanzu shine fim din kallo.
Balala ya jinjina wa jagoran shirin Aminu Saira in da ya yaba masa bisa kirkiro irin wannan kasaitaccen shiri
” Duk inda ka ga Aminu Saira ya gilma a ko ina ko shiri toh ina tabbatar maka da cewa wannan shiri zai kasaita. Aminu gwarzo kuma jarumi ne a harkar shirya wa da tasara wasan kwaikwayo, wannan shine ya sa za ka ga tare da shi zakakumai ne wadanda suka kware a aikin su daga farko har karshe. Dalilin da ya sa kenan kuka ga muna tare a koda yaushe a wajen aiki.
” Yanzu muna daukar ci gaban shirin Labarina ne. Nine kuma nake jagorancin daukan shirin. Muna amfani da Kamarori masu kyan gaske ne kuma na zamani.
Daga nan sai Balala ya shawarci matasa masu tasowa musamman wadanda suke koyan yadda a ke daukar hotuna da bidiyo cewa dole fa sai sun maida hankali matuka wajen koyon sana’ar daukan hoto da bidiyo idan suna son zama gwanaye.
Jajircewa da maida hankali a aikin daukar hoto da bidiyo shine zai kai mai koyo zama gwani. Na samu horo da dama kuma har yanzu ina cigaba da gina kaina a harkar daukar hoto da bidiyo. Ba ya ga farfajiyar Kannywood na fantsama har Nollywood inda na yi aiki da fitattun ƴan wasa kamar su AY, Zack Orji, Segun Arinze da sauransu.Kwarewa na ne ya kaini ga haka.
A karshe Balala ya bayyana cewa harkar daukan bidiyo da hotuna sunr suka kaishi ga haka, sauran kuma abinda zai yi a rayuwa nan gaba wannan na Allah ne.
0 Comments