Gwamnatin Kano ta bayyana gamsuwa da hukuncin da wata kotun majistre a jihar ta yanke na hana yin muƙabala, wato zaman tattaunawa da fitaccen malamin addinin musuluncin nan dake jihar Sheikh Nasiru Kabara.
Ranar Jumma'a ne kotun ta yanke wannan hukunci, kasa da sa'a 48 kafin gudanar da muƙabalar da aka jima ana jira.
Hukuncin ya buƙaci a tsaya a kan hukuncin da kotun ta yanke tun a ranar 8 ga watan Fabrairu, wanda ya haɗar da haramtawa Sheikh Abduljabbar yin wa'azi a jihar ta Kano.
Yayin wata zantawa da BBC, kwamishinan watsa labarai na Kano Muhammadu Garba, ya ce bayan tattaunawa da gwamnati ta yi da ma'aikatar shari'a, sun gamsu da wannan hukunci, don haka an fasa yin muƙabalar da aka shirya gudanarwa a ranar Lahadin nan.
BBC ta tambaye shi a kan zargin da wasu ke yi na cewa gwamnatin Kano na da hannu a shigar da ƙarar da aka yi don hana wannan zama, saboda yadda sarkin Musulmi ya ce baya goyon bayan a yi shi, inda ya ce kwata kwata wannan zargi ba gaskiya bane.
Ya ƙara da cewa ko da an ɗaukaka ƙara daga baya wata kotun ta ce a gudanar da zaman, sai gwamnatin Kano ta sake yin karatun ta-nutsu tukunna kafin duba yiwuwar yin hakan.
Me Sheikh Abduljabbar ya ce a kan hukuncin ?
Ɗaya daga cikin lauyoyin dake kare Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara a shari'ar Barista Rabiu Shu'aibu Abdullahi, ya ce su a iya saninsu wannan zama yana nan daram, domin babu wani waje da kotun ta fito ta ce ta hana yin Muƙabala ƙarara.
''Abun da muka fahimta da wannan hukunci shine kotu ta ce a ci gaba da aiki da hukuncin da ta yanke na ranar 8 ga watan Fabrairu. na cewa ta hana Malam Abduljabbar yin wa'azi da kuma furta kalaman tunzuri, da rufe masallacinsa da cibiyarsa, babu wani waje da tace kada a yi muƙabalar da aka shirya.
Ya ƙara da cewa kwata kwata takardar hukuncin da kotu ta yanke bashi da alaka da yin muƙabalar, ballantana a ce za a fasa yin zama.
Barista Rabiu ya ce ko da wasu na son fakewa da hana Malam Abduljabbar yin wa'azi da kotu ta yi, ''to a sani cewa ba wa'azi za a yi da Malam ba, ita gwamnatin Kano cewa ta yi tattaunawa za a yi''
0 Comments