Ticker

6/recent/ticker-posts

Saudiyya : Mayaƙan Houthi sun harbawa Saudiyya makami mai linzami

 

 
 
 
 

Saudiyya ta ce ta dakile wani hari da makami mai linzami da aka kai wa babban birninta na Riyadh wanda ta zargi 'yan tawayen Houthi da ke Yemen da kaiwa.

Rahotanni daga gidan talabijin din kasar sun ce an kuma lalata jirage marasa matuka da ke dauke da bama-bamai da ke kan hanyar zuwa biranen Kudancin Saudiyya.

Ba a bayar da rahoton asarar rai ko lalata wani abu ba sakamakon hare haren.Hare-haren wuce gona da iri kan masarautar ya karu kwanan nan yayin da kawancen da Saudiyya ke jagoranta ke ci gaba da yaki da mayakan Houthi da Iran ke marawa baya.

A wannan watan Shugaba Joe Biden ya sanar da kawo karshen goyon bayan Amurka ga yakin da Saudiyya ke jagoranta a Yemen

A karkashin shugabannin Amurka biyu na baya-bayan nan da ya gada, Amurka ta rika goya wa Saudiyya baya ne a yakin da ta ke yi da 'yan Houthi na Yemen.

Wannanrikicin ya janyo wa miliyoyin 'yan kasar ta Yemen wahalhalu da matsananciyar yunwa.

An dai fara yakin ne a 2014 tsakanin gwamnatin Yemen da kungiyar 'yan tawaye ta 'yan Houthi. Bayan shekara guda rikicin ya kara kazancewa bayan da Saudiyya da kawayenta - kasashen Larabawa takwas - da Amurka ke mara wa baya tare da Birtaniya da Faransa su ka fara kai wa 'yan Houthin hare-hare.

Amma Mista Biden ya sanar da sauyin alkibla a dangantakar Amurka da sauran kasashen duniya, wanda ya hada da wannan matakin na kawo karshen yakin

Kalaman Mista Biden sun yi hannun riga da na mutumin da ya gada - tsohon shugaba Donald Trump wanda ya sauka daga mukaminsa a watan jiya.

 
 
 
 
 

Post a Comment

0 Comments