Ticker

6/recent/ticker-posts

An sako 'yan matan makarantar Jangebe a Zamfara


 

Gwamnatin jihar Zamfara a Najeriya ta tabbatar da sakin ƴan matan makarantar Jangebe da ƴan fashin daji suka sace.

Gwamnatin ta ce ƴan matan su 279 da aka sace sun shaƙi iskar ƴanci bayan ƙoƙarin da aka yi na ganin sun kuɓuta sannan dukkansu suna cikin ƙoshin lafiya.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne ƴan fashin daji suka kutsa cikin makarantar tare da sace su.

Da sanyin safiyar Talatar nan BBC ta tattauna da gwamna Bello Matawalle na jihar ta Zamfara kuma ga ƙarin bayanin da ya yi:

"Alhamdu lillahi, mun ci nasara ga su an sako su dukansu. Dama guda 279 ne, kuma ga shi yanzu suna shigowa, yanzu muke karbar su da ni da mai dakina. Ga su suna shiga gidan gwamnati yanzu ga baki ɗaya."

Wane hali ƴan matan ke ciki?

Gwamna Mutawalle: Ga su nan lafiyarsu lau. Kun ji maganganunsu, an kara muku su kun ji su suna magana.

"Saboda haka bukatar mu dama ita ce Allah ya dawo mana da su cikin koshin lafiya, kuma ga su nan sun dawo babu wani abu da ya same su, babu kuma wadda ta halaka cikinsu.

To ko an biya kuɗin fansa kafin aka sako su?

Gwamna Mutawalle: Babu abin da aka biya. An yi komai ne bisa tattaunawar da muka yi da waɗanda su ka shiga tsakani aka yi sulhu.

"Yanzu su ma gasu nan su wajen talatin da wani abu da suka tafi suka tarar da wadanda su ka sace 'yan matan, sun yi maganganu da su kuma suka amso mana su.


'Farin ciki ya lulluɓe mu ba a yi wa yaran fyaɗe ba'

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Zamfara Abubakar Dauran ya shaida wa BBC Pidgin cewa farin ciki ya lulluɓe gwamnati saboda ƴan bindigar ba su yi wa ko ɗaya daga cikinƴan matan nan fyaɗe ba a lokacin da suke tsare a hannunsu.

"Abin da muka fara yi bayan da muka karbi yaran shi ne tambayarsu ko wani abu ya same su da suke buƙatar kulawar gaggawa, cikin sa'a sai muka tabbatar da cewa ba su taɓa ko ɗaya daga cikinsu ba, sai farin ciki ya cika mana ciki."

Sai dai kwamishinan ya ce duk da haka sun gayyaci ma'aikatan lafiya da su zo su fara duba yaran nan ɗaya bayan ɗaya ba tare da ɓata lokaci ba a nan asibitin Gidan Gwamnati da ke Gusau.

 

Post a Comment

0 Comments