Ticker

6/recent/ticker-posts

Sojojin Nijeria Sunyi Nasara A Dajin Timbuktu

 Dakarun sojin Najeriya ƙarƙashin Shirin Lafiya Dole mai yaƙi da Boko Haram sun yi luguden wuta a Timbuktu, wani ɓangare mai sarƙaƙiya a dajin Sambisa da yankunan kusa da Tafkin Chadi.



Rahotanni sun ce sojoji sun kwashe tsawon mako guda suna ɗauki-ba-daɗin fatattakar 'yan ta-da-ƙayar-baya a yankin, abin da kuma ya yi sanadin mutuwar gomman 'yan Boko Haram.


Bayanai sun ce Dajin Timbuktu, wanda ya ratsa tsakanin jihohin Borno da Yobe, ya yi ƙaurin suna don kuwa a tsawon shekara huɗu da suka gabata, sojoji sun gaza shigarsa ta ƙasa.


Sai dai a yanzu ga dukkan alamu ta faru ta kare, ƙoƙarin haɗin gwiwar sojojin Sashe Na Biyu da kuma dakaru na musamman daga sojin ƙasa na Najeriya, da haɗin gwiwar sojojin sama da ayyukan sa ido a kan kai-komon abokan gaba, ya wanzar da kyakkyawan sakamako.


Bayanai sun ce aikin fatattakar wanda ke ci gaba da gudana ya yi sanadin 'yantar da Buk da Talala da Gorgi waɗanda dukansu tungar 'yan Boko Haram ne da ke da ƙarfi.


Jaridar PRNigeria ta ce samamen ya sa ala dole, ba girma ba arziki kwamandojin Boko Haram, irin su Ameer Modu Borzogo da Modu Sullum sun tsere daga yankin.


Post a Comment

0 Comments