Tuni wasu wuraren kasuwanci a Najeriya suka buɗe tare da ci gaba da harkokinsu a karon farko, bayan kammala bikin kirsimeti da na sabuwar shekara.
Lokacin aiki kamar yadda aka saba shi ne Litinin zuwa Juma'a, amma saboda yanayin da ake ciki na annonar korona abubuwan za su ɗan sauya, a dai dai lokacin da gwamnati ke ci gaba da sanar da sabbin matakan taimakawa wuraren kasuwanci don hana bazuwar cutar.
Ga wasu daga cikin matakan da gwamnati ta ce dole ne a cika:
Ga ofisoshin gwamnati, ma'aikatan da ke kasa da matakin albashi na 12 ba za su ci gaba da aiki ba, sai in har aikin nasu ya zama tilas
Dole ne a tanadi sinadarin goge hannu a wuraren kasuwanci da kuma ofisoshi
Dole ne kuma su riƙa sanya ma'aikatansu amfani da takunkumi a kowanne lokaci
Su kuma riƙa tabbatar da amfani da tsarin nesa-nesa da juna musamman ta tsarin zama ga ma'aikata da masu ziyara
A kuma riƙa duba yanayin ma'aikata da masu ziyara a wajen ofis yayin da ake shiga
Sannan a samar da wurin wanke hannu a kai a kai da sabulu da ruwa har tsawon sakan 20
A samar da tsarin nisantar juna a ofis domin kiyaye lafiyar ma'aikata
Inda ma'aikata ke gaba da gaba da kwastomomi wajibi ne a samar musu da kayan kariya don kare lafiyarsu
Tabbatar da cewa ma'aikatan sun san yadda za su gano alamomin ƙwayar cutar korona kuma sun sami cikakken fahimta game da abin da za su yi yayin rashin lafiya da kuma karfafa musu gwiwa su zauna a gida
A riƙa nuna alamun yin kira ga jama'a su kiyaye a ofisoshin da ma'aikatu
0 Comments