Ticker

6/recent/ticker-posts

Saudiyya Zatayi Birni Mara Hanyar Mota.

 

Saudiyya ta sanar da cewa za ta fara ginin birnin da babu hanyar mota. Za a fara aikin gina birnin ne a watanni hudu na farkon wannan shekara ta 2021.

Duk wata hanya ta sufurin al'umma ko kaya za ta kasance ne ta karkashin kasa.


Yarima bin Salman ya sanar da aniyar fara aikin ne a wani bayani da ya gabatar ranar Lahadi.


A cewar yariman na Saudiyya Mohammed bin Salman, nan da shekara ta 2050 mutane biliyan daya za su rasa matsuguni saboda yawaitar hayaki mai dauke da sanadarin carbon da ke gurbata muhalli da kuma cikowar teku.


Saboda haka ne kasar ta Saudiyya ta shirya gina wani katafaren sabon birni wanda zai kasance babu motoci ko kuma titunan kwalta.


Bayanin ya nuna cewa mutum miliyan guda ne za su rinka rayuwa a birnin.


Kashi 90 cikin 100 na al'ummar duniya na shakar gurbatacciyar iska.


Ya ce "Me ya sa duniya za ta bari mutum miliyan 7 su rinka mutuwa kowace shekara sanadiyyar gurbacewar muhalli?"


"Yayin da wasu miliyan 7 din kuma ke mutuwa sanadiyyar hadurran ababen hawa."


Shirin gina birnin wanda aka yi wa lakabi da 'The Line' zai samar da birni wanda zai kunshi abubuwa ne marasa gurbata muhalli.


Birnin wanda za a rinka taka sayyada, za a samar masa da makarantu, da asibitoci, da lambuna, da kuma hanyar sufuri mai saurin gaske.


A yadda aka tsara, tafiya daga farko zuwa karshen birnin mai tsawon kilomita 170 ba za ta wuce minti 20 ba.


Post a Comment

0 Comments