Gwamnatin jihar Kaduna ta yi gargadin cewa cikin kayan abincin da aka yashe daga dakin ajiyar abinci da ke Narayi a Karamar Hukumar Chikun akwai wadanda sun lalace da wadanda aka haramta amfani da su da kuma wadanda cinsu ka iya zama haɗari.
Wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Samuel Arwan ya fitar, ta ce Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta ce ta sanar da gwamnati game da haɗarin da ke tattare da wadannan kayan abincin.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi gargaɗi cewa abincin tamkar guba yake domin zai iya haifar da rashin lafiya ga wanda ya ci ko kuma ya kashe shi ba ki ɗaya.
Ta kuma ƙara da cewa wani kamfani da ke samar da abinci, wanda aka yashe masa kayayyaki ya bayyana cewa hatsinsa da aka sace gauraye yake da wasu sinadarai da ake amfani da su domin ajiye kayan abinci wadanda ka iya illata ɗan Adam.
Sanarwar ta yi kira ga al'umar jihar da su kasance masu lura kan abinci da magungunan da za su riƙa saya da kuma asalin inda aka samo su domin kauce wa faɗawa wannan haɗari.
Gwamnatin jihar ta kuma roƙi mutane da su ba ta bayanan wadanda suka sace kayayyakin da kuma wuraren da suka ɓoye su.
A ranar Asabar ne wasu mazauna jihar Kaduna suka far wa ɗakunan ajiyar abinci na gwamnati domin neman kayan tallafin annobar korona.
Sun kwashi kayan abinci da hatsi da kujeru da wasu kayan wutar lantarki masu yawa.
Hakan ya janyo an sanya dokar hana fita a ƙananan hukumomin Chikun da Kaduna ta Kudu, daga baya kuma aka mayar da dokar a faɗin jihar baki ɗaya domin tabbatar da doka da oda.
Source: BBC Hausa
0 Comments